Connect with us

News

Shattima  `Obasanjo Da Wasu Manyan Jiga Jigai A Siyasar Nageriya Ne Suka  Halarci  Daurin Auren Yar Gidan Kwankwaso

Published

on

FB IMG 1731767513135

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

A yau Asabar aka daura Auren Yar gidan tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso da Dan gidan hamshakin Dan kasuwa Dahiru Mangal.

 

Advertisement

 

 

 

Mataimakin shugaban kasa Alhaji Kashim Shettima da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa da Gwamnan Jihar katsina Alhaji Umar Dikko Radda da wasu manyan baki sun halarci daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso.

Jaridar Inda ranka ta ta rawaito cewa diyar Kwankwaso Mai suna A’isha, ta auri Fahad Mangal, dan hamshakin dan kasuwa, Katsina Alhaji Dahiru Mangal.

Daurin auren wanda ya gudana a fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a ranar Asabar ya samu halartar manyan baki a sassa daban daban dake fadin Kasar nan.

Advertisement

 

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito mataimakin shugaban kasa Shettima ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 10:00 na safe, yayin da Obasanjo ya iso da misalin karfe 9:30 na safe sanye da farar babbarriga da jar hula, alamar tafiyar siyasar Kwankwasiyya da Kwankwaso ya bullo da shi a shekarar 2011.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Akwa Ibom da Sokoto, Ahmed Makarfi, Victor Attah da Aminu Tambuwal.

Sauran manyan baki sun hada da ministan tsaro, Abubakar Badaru, dan marigayi shugaban kasa, Muhammad Sani Abacha da Manjo Hamza Al-Mustapha.

Daurin auren ya kuma samu halartar sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na kasar nan

Tuni dai aka daura auren a fadar sarkin Kano Wanda kuma babban limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddin ya jagoranta.

Advertisement

Ango ya bayar da Naira miliyan daya a matsayin sadakin aure ya kuma bayar da kyautar Naira miliyan daya ga limaman da suka gudanar da bikin.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending