Connect with us

News

Bikin Hawan Daba A Kano Ya Shiga Kundin Tarihin Hukumar UNESCO

Published

on

Bikin hawan daba a Kano ya shiga kundin tarihin UNESCO

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar ilimi da kimiya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta saka hawan Daba na Kano a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya.

Advertisement

Hawan Daban da ake gudanarwa a jihar Kano  sau biyu a shekara a yayin bikin Sallah babba da karamar Sallah, ya samu shiga matakin ne bayan kwakwaran nazari kan abubuwan al’ada masu dumbin tarihi da ke tattare da shi.

Manyan Motocin Daukar Kaya Za Su Daina Shigowa Kano Da Rana — Gwamnatin Kano

Mai magana da yawun hukumar ilimi da kimiya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Hajo Sani ce , ta bayyana cewa bikin na samun dumbin mahalarta daga sassan kabilu daban daban, kama daga Hausawa da Fulani da Yarbawa da Bugaje da ke da zama a kasar Hausa.

Advertisement

A tsakiyar watan Yunin wannan shekarar ta 2024, hukumomin ‘yan sanda a Kano sun dakatar da hawan Daban, bisa abubuwan da suka kira shawo kan matsalolin tsaro mai nasaba da darewar masarautar Kanon gida biyu.

 

Advertisement

DW 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending