Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Wasu Mutum Biyar Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Kano

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Babbar kotun jihar Kano, mai lamba hudu karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wasu mutane 5, wadanda kotun ta samu da laifın hada baki da kisan kai.

Advertisement

Tunda fari gwamnatin jihar Kano ce ta gurfanar da mutanen a gaban kotun, da ake zargin su da hada baki da kisan kai.

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Lura Da Ayyuka Na Mutum 6 Ƙarƙashin Jagorancin Ma’aji Sumaila

Kunshin zargin da ake musu tun da fari ya bayyana cewar, a ranar 3 ga watan 9 na shekarar 2023 wata mata Mai suna Nadiya Ibrahim ta bayyana wa mai gidanta Faisal Yahaya cewar, ta yi mafarkin cewar wata makociyarsu mai suna Tsahare Abubakar ta biyo ta da wuka, bayan da ta farka kuma sai ta kama rashin lafıya.

Advertisement

Har ila yau, kunshin tuhumar ya bayyana cewar, Faisal ya yi zargin Tsahare mayyace, don haka ya gayyato wasu matasa 4 su ka bi Tsahare har gona suka daddatsa ta har sai da rai ya yi halinsa.

A yayin sauraron Shaidu lauyan gwamnati Barrister Lamido Abba Soron Dinki, ya gabatar da shaidu 4, kuma a yau kotun ta ayyana cewar, ta gamsu da shaidun masu gabatar da kara.

Advertisement

Kotun ta ayyana hukunci kisa ta hanyar rataya akan mutanen masu suna Daluta Ibrahim, da Abudil-Aziz Yahaya, da Faisal Yahaya, da kuma Ahmad Ibrahim, sai Abdurrahman Yakubu.

Sai dai kuma wata mata da ake tuhuma ta 6 mai suna Nadiya Ibrahim, kotun ta sallame ta sakamakon an gano cewar lokacin da aka yi kisan kan ita tana gida a kwance bata da lafıya.

Advertisement

Kazalika, kotun ta kuma gargadi yan uwan Tsahare akan cewar kada su cutar da Nadiya domin kotun ta gano bata da laifi.

kotun ta kuma umarci Dagacin garin Dadin kowa da ke karamar hukumar Wudil, da su tabbatar an zauna lafıya akan wannan batu, har ma mai Shari’a Usman Na’Abba ya ce, ba a yin hukunci akan mafarki kuma idan wani ya faru da mutum sai ya tuntubi masana abin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending