Connect with us

News

Yadda Kotu Ta Tuɓe Wa Sarkin Ebira Sarauta A Kogi

Published

on

An kama lauyan bogi ana tsaka da shari'a a kotu

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Wata babbar kotu a jihar Kogi da ke zaune a Lokoja ta sauke Alhaji Ahmed Muhammed Tijani Anaje daga muƙamin Ohinoyin Ebira.

Anaje ya samu naɗin sarautar ne a watan Janairu na 2024 daga tsohon gwamnan jihar, Alhaji Yahaya Bello, kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.

Kotu Ta Yanke Wa Wasu Mutum Biyar Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Kano

Sai dai a zaman kotu da aka yi a yau Litinin, mai shari’a Salisu Umar ya bayar da umarnin dakatar da Anaje daga ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarkin Ebira.

Duk da cewa cikakken bayani kan hukuncin bai fito ba tukuna, an ruwaito cewa ƙarar da ke ɗauke da lamba HCO/05C/2024, Dr. Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutane biyu suka shigar da ita kan gwamnan jihar Kogi na da nasaba da hukuncin.

 

Advertisement

 

 

WIKKI TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending