News
Kungiyar Kwadago ta NLC Ta Dakatar Da Zanga-zangar Adawa Da Karin Farashin Kudin Kira Da Na Data
DAGA MAIMUNATU BASHIR MUSA
Kungiyar Kwadago ta NLC a Nijeriya ta dakatar da zanga-zangar adawa da karin farashin kudin kira da na data da kamfanonin sadarwa ke shirin kaddamarwa
bayan wata ganawa da wakilan gwamnati a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a daren Litinin, NLC ta yanke shawarar dakatar da zanga-zangar har sai an kammala tattaunawa.
Da yake magana da ‘yan jarida bayan taron, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa gwamnati ta amince da kafa wani babban kwamiti don sake duba karin farashin kudin kira da na data da kamfanonin sadarwa ke shirin kaddamarwa
A cewarsa, kwamitin zai ƙunshi wakilai biyar daga kowanne bangare, kuma ana sa ran zai gabatar da sakamakonsa cikin makonni biyu.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
