News
Yunƙurin Rusa Jam’iyyun Adawa Babbar Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyyar Najeriya — Farfesa Kamilu
Farfesa Kamilu Sani Fagge, fitaccen masanin kimiyyar siyasa daga Jami’ar Bayero dake Kano, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke barin jam’iyyun adawa suna komawa jam’iyya mai mulki, yana mai gargadi cewa wannan matsaya babbar barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
A wata tattaunawa da Jaridar INDA RANKA, Farfesa Kamilu ya bayyana cewa irin wannan yunƙuri na nufin murƙushe jam’iyyun adawa ne, wanda ke nuna ƙarancin juriyar siyasa da rashin mutunta bambancin ra’ayi — wani ginshiƙi na ainihin dimokuraɗiyya.
Gwamnatin Kano Ta Shirya Bita Ga Limaman Juma’a Don Karfafa Huldar Al’umma Da Gwamnati
Idan za ku iya tunawa a irin wannan hadakar ta faru a Jamhuriyar farko da ta biyu, amma ba ta haifar da ci gaba ba, illa zanga-zanga da asarar rayuka. A cewarsa, haɗa kan jam’iyyun adawa da jam’iyya mai mulki ba ya amfani da tsarin mulkin dimokuraɗiyya, illa kawai yana amfani wa wasu ‘yan siyasa da ke bin son zuciya da neman amfana da mulki.
”Kasashe da dama da suka ci gaba a fannin dimokuraɗiyya, ana samun ƙarfi da kariya daga jam’iyyun adawa masu zaman kansu, waɗanda ke zama madogara ga ‘yan ƙasa su furta takaici ko rashin gamsuwarsu da tsarin mulki,” in ji Farfesa.
Ya kara da cewa a wasu ƙasashe, rashin ingantaccen tsarin adawa kan haifar da rashin jin daɗi da rikice-rikice, har ma ya kai ga juyin mulki daga sojoji, sakamakon mamaye jam’iyya ɗaya da kuma raunin sauran jam’iyyun siyasa.
A ranar Litinin da ta gabata, Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gada, Ifeanyi Okowa, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki. Haka zalika, wasu ‘yan majalisar dokoki daga jam’iyyun adawa sun bi sahunsu — matakin da ya janyo cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya.
A karshe, Farfesa Kamilu ya yi kashedi cewa wannan yunƙurin rusa jam’iyyun adawa na iya haifar da koma baya ga tsarin zabe, rage yarda da gwamnati, da jefa ƙasa cikin rudani. Ya kuma nuna damuwa kan yadda siyasa ke komawa hanyar da mutane ke amfani da ita don son kai, ba don hidimar jama’a ba.
