News
Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Kwamiti Domin Bincike Kan Abinda Ya Faru A Rimin Zakara
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta kafa kwamitin musamman domin gudanar da bincike kan rikicin da ya faru a unguwar Rimin Zakara, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan ta bakin mai taimaka masa na musamman kan kafafen yada labarai, Bashir A. Bashir, a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai kan lamarin.
Kungiyar Kwadago ta NLC Ta Dakatar Da Zanga-zangar Adawa Da Karin Farashin Kudin Kira Da Na Data
A cewarsa, rikicin ya samo asali ne sakamakon kokarin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) na karɓar filayenta, bayan neman hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano domin dawo mata da mallakinta. Wannan mataki ne ya sa gwamnati ta shiga tsakani tare da ba wa mutanen da ke zaune a wurin wa’adin ficewa daga yankin. Sai dai kuma wa’adin da aka ba su ya riga ya cika.
Gwamnatin Kano ta bayyana matuƙar damuwa kan aukuwar rikicin, tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da duk waɗanda suka samu rauni. Binciken da za a gudanar zai tabbatar da gano musabbabin rikicin, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kauce wa faruwar irin haka a gaba.
Gwamnati na kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.
