News
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Lura Da Ayyuka Na Mutum 6 Ƙarƙashin Jagorancin Ma’aji Sumaila
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dangane da nasarorin da aka samu wajen lura da ayyukan gwamnati a fadin Jihar Kano, da kuma kokarin tabbatar da inganci sabida da kimar kudaden da aka kashe, Gwamnan Jihar Kano, Malam Abba Kabir Yusuf, ya kafa Kwamitin Lura da Ayyuka na Jihar wanda ya kunshi mutum 6.
Kwamitin yana da alhakin bibiyar ayyukan da gwamnatin jiha ke aiwatarwa don tabbatar da cewa an gudanar da su bisa ka’ida, tare da inganta ingancinsu.
Tiyatar Yoyon Fitsari: Mata 100 Sun Sami Tiyata Kyauta da Tallafin Ƙarfafawa A Kano
Membobin kwamitin sun hada da:
1. Comrade Nura Ma’aji Sumaila – Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Yadda Ake Ba da Kwangiloli da Bibiyar Ayyukan Gwamnatin Jihar (Shugaban Kwamitin).
2. Comrade Ibrahim Waiya – Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai.
3. Engr Marwan Ahmad – Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje.
4. Alhaji Ali Haruna Makoda – Kwamishinan Ilimi.
5. Hon. Nasiru Sule Garo – Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
6. Alhaji Muhammad Habibu Sale – Shugaban Hukumar Kare Ayyuka ta Jihar Kano (Kano PRO-PA).
Kwamitin ya gudanar da taron farko a ranar 1 ga Fabrairu, 2025, a Ma’aikatar Kula da Yadda Ake Ba da Kwangiloli da Bibiyar Ayyukan Gwamnatin Jihar. Taron ya kasance na fahimtar juna da kuma tsara hanyoyin aiki da manufofin kwamitin.
Daga cikin shawarwarin taron, kwamitin ya bayar da shawarar hada Kungiyoyin Farar Hula (CSOs), Kungiyoyin Cibiyoyin Al’umma (CBOs), da Kungiyoyin Sa-kai (NGOs) cikin ayyukansa, domin tabbatar da sa hannun jama’a wajen tantance ci gaba da tasirin ayyukan al’umma.
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ayyuka sama da 300 a fadin jihar, inda Ma’aikatar Ayyuka da Ma’aikatar Ilimi suka zama manyan ma’aikatun da ke kula da mafi yawan wadannan ayyuka.
Za a ci gaba da bayar da rahoto kan ayyukan kwamitin a lokuta daban-daban domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gudanar da ayyukan gwamnati.
