News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Musanta Zargin Karɓar Bashin Naira Biliyan 177 Domin Samar Da Ruwan Sha
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaryata zargin da ke cewa ta karɓi bashin ₦177 biliyan domin samar da Ruwan Sha a jihar daga ƙasar Faransa.
Gwamnatin kano ta bayyana rahoton da ya yi wannan zargi a matsayin “mugun nufi” da “ƙarya.” Wannan martanin ya biyo bayan rahotanni na dake nuna cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samu wannan bashi.
Tsadar Rayuwa: Yadda Wake Da Biredi Da Doya Suka Yi Wa Talaka Fintinkau A Najeriya
A wata sanarwa da Hamisu Sadi Ali, Darakta Janar na hukumar kula da basussuka ta Jihar Kano, ya fitar, ya bayyana cewa babu irin wannan bashi da aka taɓa karɓa. Ya jaddada cewa, bisa doka, duk wani bashi ya kamata ya bi ta hukumar kula da basussuka ta Jihar Kano kuma ya bi ƙa’idoji, musamman idan daga ƙasashen ƙetare ne.
Ali ya ƙara da cewa gwamnatin jam’iyyar NNPP tana mai da hankali kan biyan basussukan da aka gada daga gwamnatin baya. Ya ambaci yarjejeniyar bashi ta €64 miliyan da aka rattaba hannu a kai a shekarar 2018 a lokacin mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC. Wannan bashi, daga hukumar raya ƙasashe ta Faransa, an yi nufin amfani da shi domin aikin gyaran ruwan fanfo na cikin birnin Kano, inda aka riga aka fitar da €13 miliyan.
Ali ya buƙaci jama’a da su yi watsi da wannan rahoton na ƙarya, yana mai jaddada cewa aikin jarida ya kamata ya dogara da gaskiya ba ƙirƙirar ƙarya ba.
