News
Tsadar Rayuwa: Yadda Wake Da Biredi Da Doya Suka Yi Wa Talaka Fintinkau A Najeriya
Daga Watan Agusta 2023 Zuwa Agusta 2024: Waɗannan watanni 12 na shekara ɗaya cif-cif, sun zo wa talakawan Najeriya a halin da ba a taɓa tsammani ba.
Duk da dai dama an shafe dama da shekara biyu ana fafata matsin tattalin arziki, an rufta raɗaɗin tsadar rayuwa tun bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin fetur a ranar da aka rantsar da shi, wato 29 ga Mayu, 2023.
Masifar tsadar rayuwa ta ƙara muni da ta’azzara daga watan Agusta na 2023, inda daga lokacin ne kayan abinci suka daina yin tashin agwagwa mai gajeren zango, suka riƙa yin tashin-gwauron-zabo mai nisa zango. Daga nan farashi ya fara nunkawa har zuwa cikin Agusta, 2024.
Yayin da farashi ke ƙara nunkawa, a gefe ɗaya kuma farashin fetur na ƙara tashi sama kamar tashin shamuwar fita ci-rani. Hakan ya ƙara gigita rayuwar ‘yan Najeriya matuƙa.
Binciken da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar wanda aka wallafa a ranar 25 ga Satumba, 2024, ya nuna yadda farashin wake, ƙwan kaji, biredi, shinkafa, doya da sauran wasu kayan abinci ya nunnuka farashi a cikin watanni 12 na Agusta 2023 zuwa Agusta 2024.
NBS ta fitar da Ƙididdigar Wasu Ɗaiɗaikun Kayan Abinci a Watan Agusta 2024, wanda ta fitar ranar Laraba a Abuja.
Rahoton ya nuna farashin kilo 1 na wake ya nunka har kashi 271.56%, daga Naira 692.95 a cikin Agusta 2023, zuwa Naira 2,574.63 cikin Agusta, 2024.
Tsadar wake ta sa gidajen aka raina masu cin shinkafa da wake da mai, su ma ɗin cin waken ma ya nemi ya gagare ku.
Ko a cikin Abuja sai da manya da ƙananan gidajen cin abinci da yawa suka daina sayar da wake dafaffe. Haka wuraren da ake yin alala duk sun daina.
Yayin da ƙwan kajin gidan gona ya yi tsada, tashin farko bayan Agusta 2023 ya tashi da kashi 121.92 zuwa Agusta 2024.
Hakan ya na nufin kafin Agusta 2023 ana sayar da ƙwaya 12 kan Naira 1,031.55, amma zuwa Agusta 2024 ya dangana Naira 2,289.19.
Premium Times ta ruwaito cewa matasa da dama tazurai da masu ci-rani da ke cin indomi da ƙwai, suka ƙaurace masu, dama tuni ita indomi ɗin ta yi wa talaka fintinkau, kamar yadda taliya ke neman gagarar sa ci.
Doya ta yi tashin gwauron zabin da ta zama sai wane da wane, yayin da wadda a cikin Agusta 2023 ake sayarwa Naira 11, a cikin Agusta 2024 sai da ta kai Naira 36,000. Ta Naira 570 ta koma Naira 1,650 a cikin Agusta 2024.
Tumatir ɗin Naira 554 cikin Agusta 2023, shi aka riƙa saye Naira 1,500 cikin Agusta 2024. Aka bar talaka na miya da gwalagwajin ruɓuɓɓen tumatir.
Ita kuwa shinkafa dama tuni ta riƙa sa zuciyar mai ƙaramin albashi bugawa a duk ranar da ya ɗauki albashi. Saboda idan ya ce zai sayi shinkafa, to fa daga nan ko gawayin da matar sa za ta hura wuta ta dafa masa shinkafar ba zai iya saye ba.
Tilas mai ƙaramin ƙarfi ya koma ya na cin burtuntunar shinkafa, wadda a yanzu aka raɗa wa suna a-fafata. Wato a fafata a samu a kai ƙarshen wani wata, ko a fafata a ci kafin maigida ya fita ya samo abin da za a ci gobe wata safiyar ko wani daren.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
