Connect with us

News

Tsadar Rayuwar Da Ake Ciki Na Shafar Lafiyar Kwakwalwar Wasu ‘Yan Najeriya —Masana

Published

on

Faduwar Darajar Naira Da Tsadar Man Fetur Ke Ruruta Tsadar Abubuwa A Najeriya

DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Rahotanni sun ce matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa na jefa ‘yan Najeriya da dama cikin yanayin fita daga hayyacin su, abinda ka iya shafar lafiyar kwakwalwarsu.

Advertisement

Wasu masana kiwon lafiyar bil Adama a Najeriya Aisha Bubah da Jecinta Egbim suka bayyana haka, sakamakon irin halin Tsadar Rayuwa da jama’ar kasar suka samu kansu, wanda ya jefa su cikin halin kakanikayi. Rahotan ya ce cibiyoyin lafiyar Najeriya sun samu karin sama da kashi 200 na masu fama da irin wadannan matsaloli a Najeriya.

An Yanke Wa Wani Ɗan Kasar Waye  Hukuncin Shekaru 14 A Gidan Kaso A Kano

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane sama da dubu 720 ke kashe kansu da kansu kowacce shekara a duniya saboda shiga irin wannan yanayi, kuma kashi 77 daga cikin su na fitowa ne daga kasashe matalauta da kuma masu tasowa irin Najeriya.

Advertisement

Masanan sun ce Najeriya ce gaba wajen samun mutanen da yanayin tsadar rayuwa ke shafar lafiyar kwakwalwar su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending