Connect with us

News

An Yanke Wa Wani Ɗan Kasar Waye  Hukuncin Shekaru 14 A Gidan Kaso A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano ta yanke wa wani ɗan ƙasar Labanon, Zuhier R. Akar mai shekaru 67 hukuncin zama a gidan kaso  na tsawon shekaru 14 sakamakon lalata wasu yara mata biyu.

Advertisement

Hukumar hana fataucin ɗan-adam (NAPTIP) reshen jihar, ta tsare Aktar ne wanda ke zama a yankin Gidan Wanka da ke ƙaramar hukumar Fagge da laifuka biyu da ke da alaƙa da lalata.

Kar Ku Dorawa Mijina Laifi Domin Ba Shi Ya Sanyaku Cikin Matsin Rayuwa Da Kuke Fama Da Shi A Yanzu Ba  —Uwargidan Shugaban Tinubu

A lokacin gudanar da hukuncin, Mai Shari’a S. M. Shua’ibu ya ce an tabbatar da wanda ake tuhuma da aikata laifin inda ya zartar masa da hukuncin zama a Gidan Kaso na shekara 14 ba tare da zaɓi na biyan tara ba.

Advertisement

Sannan, alƙalin ya kuma umarce shi ya biya tarar Naira miliyan 2 ga  waɗanda ya aikatawa laifin.

A ranar 5 ga watan Satumba, 2024 ne hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS ta ruwaito batun ga NAPTIP.

Advertisement

Wata ɗaukar bidiyo ta nuna yadda tsohon ke lalata da wasu ƴan mata biyu masu shekaru 14 da 15 a gidansa da ke unguwar Gidan Wanka

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending