News
Kar Ku Dorawa Mijina Laifi Domin Ba Shi Ya Sanyaku Cikin Matsin Rayuwa Da Kuke Fama Da Shi A Yanzu Ba —Uwargidan Shugaban Tinubu

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sanata Oluremi Tinubu, ta ce bai kamata a zargi mijinta, Bola Ahmad Tinubu ba, kan tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.
‘Yan Nijeriya dai na cikin hali na matsin tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur wanda ya sauya farashin man fetur daga Naira 198 zuwa Naira 1,030.
Hukumomin Tsaro A Najeriya Sun Tsaurara Matakan Tsaro Tare Da Sa-ido Sosai A Birnin Kano
Yawan Kwangilolin Da Kamfanonin Kera Jiragen Ruwa Dake Aiki Da Makamashi Mai Tsabta Na Sin Suka Samu Ya Kai Kashi 70% Bisa Na Duniya
Sai dai a lokacin da take magana a fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Alhamis, Uwargidan shugaban kasar ta ce, gwamnatin Tinubu har yanzu bata gama murmurewa ba.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa Uwargidan shugaban kasar, ta je garin Ife ne domin kaddamar da dakunan kwanan dalibai da wata hanya mai tsawon kilomita 2.7 da Ooni na Ife ya bai wa Jami’ar Obafemi Awolowo, (OAU), wanda aka sanya sunanta.