News
Cututtukan Da Ba Su Jin Magani Na Yi Wa Abinci Da Kiwon Lafiya Babbar Barazana – Hukumar NCDC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta nuna fargaba da gargaɗin cewa akwai buƙatar yin gaggawar shawo kan cututtuka waɗanda ba su jin magani (AMR), domin barazana ne sosai ga duniya baki ɗaya.
Darakta Janar na NCDC, Jide Idris ne yw bayyana haka a ranar Litinin, lokacin da yake jawabi a Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 79 (UNGA79), kan kiwon lafiya, wanda MSH suka shirya.
Ambaliyar Ruwa: Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Tallafin N300bn Ga Al’ummar Maiduguri
“AMR fa ba abin yi wa riƙon sako-sako ba ce. Barazana ce gagarimar gaske ga duniya. Su cututtukan da ba su jin magani su na yi wa tsarin abincin mu da hanyoyin gudanar abinci a cikin jiki barazana. Kuma barazana ne ga lafiyar ƙananan yara, su na kawo cikas ga tattalin arzikin ƙasa, kuma su na gurgunta matakan tsaron ƙasa.” Inji shi.
Shugaban na NCDC ya ci gaba da cewa idan ba a shawo kan matsalar a cikin gaggawa ba, to miliyoyin mutane fa za su talauce, su afka cikin masifar fatara da raɗaɗin tsadar rayuwa. Kai za a iya ma kashe miliyoyin mutane a duniya.”
Premium Times
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
