Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano tace ta Gano Manyan Matsalolin Makabartun Jahar.

Published

on

Alhaji Hamza Safiyanu Kachako

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata dauki matakan magance manyan matsalolin da makabartu ke fuskantar a cikin kwaryar birnin jihar.

Shugaban kwamitin kuma kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaba al’umma Alhaji Hamza Safiyanu Kachako shi ne ya bayyana haka ne jim kadan bayan samun rahoto daga shugabannin da suka zagaya makabartun domin tantance matsalolin.

Advertisement

Yan sanda sun hana amfani da gilashin mai kala da kuma rufaffiyar lamba a Borno

Ya ce zagayen ya gano rashin ingantacciyar Katanga da magudanar ruwa da fitulun tsaro da rijiyoyin burtsatse, masu gadi da dai sauransu amatsayin manyan matsaloli ga makabartu.

Hamza Safiyanu Kachako ya kara da cewa ma’aikatar za ta mika rahoton ga gwamna Abba Kabir domin amincewar sa.

Advertisement

Daga nan sai ya bada tabbacin gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen inganta yanayin makabartu.

Kwamishinan ya gargadi mutane da su guji zubar da shara a makabartu.

Advertisement

Daga cikin wuraren da aka ziyarta akwai makabartar Gama da Unguwa Uku DA Tarauni da kuma Court Road.

Sauran sun hada da makabartar Gandun Albasa da ‘Dan Agundi da Hauren Shanu dake karamar hukumar Gwale.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending