News
Yan sanda sun hana amfani da gilashin mai kala da kuma rufaffiyar lamba a Borno
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce an hana amfani da gilashin mai kala da kuma rufaffiyar lamba a motoci a jihar.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Kamiludeen Sani, kakakin rundunar ‘yan sandan, ya ce an kuma hana amfani da lambar da aka rufe a jihar.
Cikekken bayani kan matakin da gwamnati jigawa ta dauka a kan shugabannin asibitin gumel
Sani ya ce rundunar ta lura da yadda masu ababen hawa ke amfani da gilashin abin hawa, rufaffiyar lambobi da lambobin leƙen asiri ba gaira ba dalili.
Ya ce rundunar ‘yan sandan ta kuma lura da cewa wasu mutane da ba su ba da izini wajan amma fani da ita a jihar.
Kakakin ya gargadi mazauna yankin kan yin irin wannan aika-aikar, inda ya kara da cewa ba za a amince da ayyukan da suka saba wa doka ba.
Jaridar cable ta rawaito cewa An gargadi wadanda suka karya doka kan amfani da kayan da su daina saboda ‘yan sanda ba za su bari marasa kishin kasa su karya doka ba ta hanyar rashin bin doka da oda.
“An umurci dukkan shugabannin ma’aikatu, kwamandojin yanki, jami’an ‘yan sanda na yanki da kwamandojin dabarun yaki da su kara sanya ido a yankunansu.
“An kuma umurce su da su hada kai da sauran hukumomin tsaro don raba bayanai da rahotannin sirri da kuma tabbatar da hadin gwiwa wajen aiwatar da dokar da kuma magance duk wata barazana da ta kunno kai.”
A shekarar 2021, Usman Baba, tsohon sifeto-Janar na ‘yan sanda, ya bayar da umarnin dakatar da bayar da izinin yin amfani da gilashin kala-kala da lambar SPY ga motoci a fadin kasar nan.
Daga baya Baba ya kebe motoci masu gilashin masana’anta daga haramcin.
