Connect with us

News

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Akan Zanga-Zanga – NLC

Published

on

ƙungiyar ƙwadago ta NLC na Zanga zanga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ce zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da ta shirya farawa a yau Laraba na nan daram.

Ƙungiyar na mayar da martani ne bayan wasu rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar ta janye shirin nata bayan ganawa da wakilan gwamnati a yammacin jiya Talata.

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Akan Zanga-Zanga – NLC

Cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta wallafa a shafukan ta na sada zumunta, kungiyar ta ce

“Wannan ganawar ba ta sauya komai ba game da abin da muka tsara a matsayi. Muna tabbatarwa cewa zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya za ta fara a ranar [Laraba].”

Advertisement

Sanarwar ta yi kira ga ‘ya’yan ƙungiyar su taru a jihohinsu don gudanar da zanga-zangar “da zimmar yin magana da murya ɗaya”.

Tun da farko, Muƙaddashin babban sufeton ƴan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya bayana damuwa kan zanga-zangar da ƙungiyyin ƙadagon suka shirya yi, inda ya yi gargaɗin cewa ƴan sanda ba za su lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce ƴan ƙasa suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya yi tanadi amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ƴan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zanga tana rikiɗewa ta zama tashin hankali, saboda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.

ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.

A bangaren zaman kan tebur, an tashi ba tare da cimma matsaya ba tsakanin bangaren kungiyar da kuma na gwamnati.

Advertisement

Kungiyar ta nanata cewa, baza ta janye kudirin nata ba, har sai gwamnatin tarayya ta janye manufofin ta, da kungiyar ta ce sun jefa al’ummar Najeriya cikin azabar radadin rayuwa

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending