News
Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Ta Sake Fatali Da Tayin N57,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta sake yin watsi da tayin naira 57,000 a matsayin mafi ƙarncin albashi a ƙasar da kwamitin ƙarin albashin ya yi mata.
Wannan ne karo na uku da NLC ke watsi da ƙarin da gwamnatin ta yi masa cikin kusan mako guda.
Majalissar Dokokin Kano ta amince da rusa masarautu hudu da aka kirkira
A ranar Talata ne NLC ta yi watsi da tayin naira 54,000 da gwamnatin ƙasar ta yi wa ma’aikatan ƙasar, bayan da a makon da ya gabata ƙungiyar ta ƙi amincewa da tayin naira 48,000 daga ɓangaren gwamnatin ƙasar.
Ƙungiyar dai ta bai wa gwamnatin ƙasar wa’adin zuwa ranar 31 ga watan Mayun da muke ciki domin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashin.
Advertisements
