News
Zargin Damfara: ’Yan Kasuwar Waya Na Farm Center Sun Kulle Shagon Anas Magu
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kano – ’Yan kasuwar waya a shahararren kasuwar Farm Center sun kulle shagon Anas Magu, wanda aka fi sani da mai sayar da waya ta intanet, bisa zargin damfara.
Rahotanni sun nuna cewa wasu kwastomomi da abokan kasuwancinsa sun yi korafin cewa yana sayar da wayoyi ta hanyar intanet, amma daga bisani bai cika alkawarin kai wa kwastomomi kayansu ba.
‘Dan Afghaninstan Ya Raunata Masu Zanga-zangar Lumana Kusan 30 Da Mota A Jamus
Wannan ya haifar da fushi a tsakanin ’yan kasuwa, wadanda suka dauki matakin kulle shagon nasa har sai an warware matsalar.
Shugaban ’yan kasuwar Farm Center ya bayyana cewa suna kokarin fahimtar hakikanin abin da ke faruwa kafin su dauki mataki na gaba.
A halin yanzu, Anas Magu bai yi cikakken bayani ba kan zargin da ake masa, amma ana sa ran hukumomi za su shiga tsakani domin warware rikicin.
