News
Ranar Rediyo Ta Duniya A Shekarar 2025: Sako Zuwa Ga Matasa ‘Yan Jarida
A yayin da muke bikin Ranar Rediyo ta Duniya a wannan shekara ta 2025, Ina so na yi amfani da wannan dama domin tunatar da abokan aikina musamman mu matasa ‘yan jarida irin karfi da tasirin Rediyo.
Rediyo ta canza rayuwar miliyoyin mutane kuma har yanzu tana ci gaba da Inganta al’umma da daidaikun mutane da zama wani tsani tsakanin shugabanni da wadanda ake mulka.
Zargin Damfara: ’Yan Kasuwar Waya Na Farm Center Sun Kulle Shagon Anas Magu
Idan muka yi aikin jarida bisa sadaukarwa, mutuntawa, da gaskiya, ba wai kawai muna bada labarai domin sanar da mutanen halin da ake ciki ba, muna tasiri wajen samun sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.
Muryoyin mu suna da tasirin ilmantarwa, zaburarwa, da Inganta zamantakewar al’umma.
A faggen wannan aiki, gaskiyar da muke ganowa da kuma bayyanawa ta wuce bayanai kawai, nauyi ne da kuma hidima ga al-umma.
Nasan cewa akwai kalubale, amma mu jajirce domin kasancewarmu matasa muna da lokaci sosai da za mu yi wannan sadaukarwa.
Ya ’yan uwana matasa ’yan jarida mu tuna cewa duk wani labari na gaskiya da muka bayar da duk wani aikin alkhairi ba za su tafi a banza ba.
Ko da babu wanda yake kallo ko yabawa, Allah yana sane da niyyarmu da ayyukan mu kuma idan muka sadaukar da kanmu ga adalci, gaskiya, da kyautata rayuwar al’umma, za mu sakamako ba a nan duniya kadai ba, har ma a Lahira.
Ni da kaina, rediyo ta sauya tunanina ta bangarori da dama kuma ta sauya rayuwata.
Mu ci gaba da amfani da muryoyin mu wajen kyautata wannan aiki na Jarida, domin sakamako ayyuka na gaskiya ka iya ceto al-umma ko daidaikun mutane daga wani kangi ko matsala.
Mu jajirce, mu kasance masu gaskiya, kuma muryar mu ta zama mai ƙarfi domin samun ingantaccen sauyi.
Ba ka iyawa, ba a yabawa, kuma baka gamawa.
Barka da Ranar Radiyo ta Duniya!
Nura Haruna Mudi
‘Dan Jarida.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
