Business
Yan kasuwar Kano sun bukaci ƙara wa’adin daina karbar tsoffafin kudi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
‘Yan kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano, sun koka kan yadda harkokin cinikinsu ya ja baya, sakamakon yadda wa’adin daina karɓar tsofaffin Kuɗin Naira (N1000, N500, N200) ke cigaba da kusantowa.
Tuni wasu yan kasuwar suka fara sanar da abokan huldar su cewa za su daina karbar tsofaffin kudin daga yau Asabar, yayin da wasu kuma suka ambata ranar Litinin da kuma Talatar makon gobe ko Laraba, sai dai a tura musu ta asusun ajiya na banki (transfer).
Yan kasuwar ta bakin sakataren ƙungiyar masu sana’a a waje ta kantin kwari, Musa Arzai, ne bayyana haka ga manema labarai, inda yace suna bukatar a ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin Kuɗin da babban bankin Nigeria CBN ya ayyana ranar 31 ga watan da muke ciki na Janairu a matsayin cikar wa’adi.
