Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Wata Mata Mai Shekaru 40 Da Robobin Hodar Iblis 424 A Kano

Published

on

NDLEA Ta Kama Wata Mata Mai Shekaru 40 Da Robobin Hodar Iblis 424 A Kano

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama wata mata mai suna Khadijah Abdullahi mai shekaru 40 dauke da kwalaben maganin tari mai sinadarin Hodar Iblis har guda 424 a jihar Kano.

An cafke Khadijah ne a unguwar Lungun Bulala Yalwa a ranar Talata, 18 ga Maris, bayan bincike na musamman da jami’an NDLEA suka gudanar kan ayyukan fataucin miyagun kwayoyi a yankin.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirinta na Kawar da Cutar Tarin Fuka Nan Da Shekarar 2030

A wata sanarwa da Daraktan yada Labarai na NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, hukumar ta bayyana cewa wannan kamen wani bangare ne na kokarin hana yaduwar shaye-shaye da fataucin kwayoyi a Najeriya.

Haka nan, a wani samame da aka yi a ranar Alhamis, 20 ga Maris, jami’an NDLEA sun cafke wani mutum mai suna Michael Ogundele mai shekaru 45 dauke da cilindar gas na karfe mai dauke da kwayoyin tramadol har guda 50,000 a Tamburawa, kan hanyar Zaria-Kano.

Advertisement

Hukumar NDLEA ta nanata kudurinta na ci gaba da yakar fataucin miyagun kwayoyi da kuma wayar da kan al’umma ta hanyar shirin War Against Drug Abuse (WADA).

Shugaban hukumar, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd), ya yaba wa jami’an da suka gudanar da wadannan kama-kamai, tare da jaddada cewa NDLEA ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da safarar kwayoyi da kuma rage yawaitar shaye-shaye a Najeriya.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending