Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Yan Arewa A Edo, Ta Nemi Ayi Adalci

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana matuƙar damuwarta tare da mika ta’aziyyarta ga iyalai da abokan wadanda suka rasa rayukansu a mummunan harin da ya faru a Uromi, Jihar Edo.

A cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin ta bukaci a gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa domin gano masu hannu a wannan ta’addanci tare da hukunta su bisa doka. Haka kuma, ta jaddada cewa dole ne a dauki mataki kan duk wani jami’in tsaro da ya kasa cika nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sarki Aminu Ado Bayero Ya Samu Lambar Girmamawa A Matsayin Sarki Mafi San Zaman Lafiya A Najeriya.

Gwamnatin Kano ta tunatar da hukumomin Najeriya cewa suna da hakkin doka da na kasa da kasa wajen kare rayuka da ‘yancin kowane dan kasa.

Saboda haka, gwamnatin ta yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, da su fito fili su yi Allah-wadai da wannan ta’asa tare da daukar matakan tabbatar da adalci. Ta bukaci a gurfanar da duk masu hannu a kisan a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

Gwamnatin Kano ta jaddada kudurinta na mara baya ga duk wani yunkuri da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending