News
Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Musanta Labarin Kona Mota Dauke Da ‘Yan Kabilar Igbo
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kai hari ga wata mota mai dauke da fasinjoji ‘yan kabilar Igbo a Kano.
A cewar rundunar, wannan labari ba gaskiya ba ne, kuma ana neman hana yada irin wadannan rahotanni marasa tushe.
Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Yan Arewa A Edo, Ta Nemi Ayi Adalci
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta zo ne kwana kadan bayan harin da aka kai wa wasu matafiya ‘yan Arewa a Uromi, Jihar Edo, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16.
Rundunar ‘yan sandan ta ce zuwa yanzu ta kama mutane 14 da ake zargi da hannu a wannan lamari, kuma ana ci gaba da bincike.
Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su guji yada labaran karya, masu haddasa firgici da rura rikici a cikin al’umma.
Rundunar ta tabbatar da cewa tana aiki tukuru domin kare lafiyar dukkan mazauna jihar ba tare da la’akari da kabilarsu ko addininsu ba.
Haka kuma, an yi alkawarin gudanar da cikakken bincike domin gano tushen wannan karya, tare da daukar matakin doka kan wadanda suka kitsa shi.
‘Yan sanda sun bukaci jama’a da su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk wani mutum ko kungiya da ke yada labaran karya zuwa ga hukumomin tsaro mafi kusa.
