News
Da Dumi-Dumi An ga watan sallah a Saudiyya, gobe Lahadi sallah
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal, wanda hakan ke kawo karshen azumin watan Ramadana na shekarar 2025.
Jaridar INDA RANKA ta rawaito shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da ganin watan a yammacin Wannan rana.
Sanarwar ta ce gobe lahadi ita ce zata zama 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446.
Advertisements
