News
Usman Salisu Dausayi Ya Taya Alhaji Abba S. Dan Awwade Murnar Barka Da Sallah
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Usman Salisu Dausayi, babban hadimi kuma masoyi ga Shugaban Young Traders and Political Alliance na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Malam, ya taya Alhaji Abba S. Dan Awwade, Shugaban Kananan ‘Yan Kasuwa da Wayar da Kai, murnar Barka da Sallah.
A cikin wata sanarwa da ya aikowa jaridar Indaranka, Usman Salisu Dausayi ya jinjinawa Alhaji Abba S. Dan Awwade bisa kyakkyawan tsarin shugabancinsa da nagartaccen hulɗa da al’umma, musamman ma kananan ‘yan kasuwa masu tasowa.
Da Dumi-Dumi An ga watan sallah a Saudiyya, gobe Lahadi sallah
Dausayi ya bayyana cewa shugabancin Dan Awwade ya kasance na adalci da mutunta kowa da kowa, yana kuma inganta yanayin kasuwanci da rayuwar kananan ‘yan kasuwa a Jihar Kano.
“A hakika, an ajiye gwarya a gurbinta. Dan Awwade yana da gogewa da kyawawan halaye na shugabanci, yana girmama manya da kuma kula da ƙanana,” in ji Dausayi.
Ya ƙara da cewa kananan ‘yan kasuwa da ke karkashin jagorancin Dan Awwade suna jin daɗin kasancewa da shi sakamakon kyakkyawar kulawarsa da irin goyon bayan da yake basu.
A madadin kananan ‘yan kasuwa na Jihar Kano, Usman Salisu Dausayi ya taya Alhaji Abba S. Dan Awwade, iyalansa, da daukacin al’ummar Musulmi murnar bikin Sallah, yana fatan Allah ya ƙara albarka da zaman lafiya.
