News
Kisan Edo: Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Musamman Don Tattaunawa Da Gwamnatin Jihar Edo
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana matuƙar bakin ciki kan mummunan lamarin da ya faru a Jihar Edo, wanda ya yi sanadin rasa rayukan bayin Allah da yawansu ‘yan asalin Kano ne. Wannan lamari ya haifar da damuwa matuƙa ga gwamnati da al’ummar jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa kwamitin musamman da zai garzaya zuwa Jihar Edo domin tattaunawa da gwamnatin jihar da nufin binciko waɗanda suka aikata wannan danyen aiki tare da tabbatar da an samu adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Usman Salisu Dausayi Ya Taya Alhaji Abba S. Dan Awwade Murnar Barka Da Sallah
Lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mafarauta suka taho daga Jihar Ribas domin zuwa Kano yin bikin Sallah tare da iyalansu, inda wasu ƴan bijilante da wasu matasa ɗauke da makamai suka tsare su, sannan suka musu duka tare da ƙone su baki ɗaya.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiyaya, ya fitar.
Sanarwar ta yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani abu da ka iya haddasa rikici.
Bugu da ƙari, Gwamnatin Kano ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan tare da yin addu’ar Allah ya jikan su.
