Connect with us

News

Jaridar Inda Ranka Na Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Ƙaramar Sallah.

Published

on

IMG 20250330 WA0006

Bayan kammala Ibadar Azumin Watan Ramadan na shekarar 1446 bayan hijirar Annabi Muhammad (S.A.W.)Daga Makkah Zuwa Madina, Jaridar Inda Ranka Na Taya al’ummar Musulmin Duniya Murnar Zagayowar Bikin Ƙaramar Sallah.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Jaridar, KABIRU BASIRU FULATAN, Ya Sanyawa Hannu A Ranar Asabar, Jaridar Ta Bayyana Gaodiyarta Ga Allah tare Da Fatan Alheri Ga Al’ummar Musulmi Baki Ɗaya.

Advertisement

Kisan Edo: Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Musamman Don Tattaunawa Da Gwamnatin Jihar Edo

Fulatan Ya Kuma Jaddada Cewa Inda Ranka Jarida Ce Dake Da Burin Cigaban Addinin Musulunci, Tare Da Gabatar Da Hirarraki Da Manyan Malamai Domin ilmantar Da Al’umma Da Kuma Shiryar Dasu Zuwa Ga Rabauta A Ranar Gobe Ƙiyama.

Haka Zalika, Jaridar Tana Kira Ga Al’ummar Najeriya Dasu Cigaba Da Haɗa Kai Wajen Yin Aiki Tuƙuru Domin Samun Yardar Allah, Ƙaruwar Zaman Lafiya, Da Yalwar Arziƙi. “Najeriya Ƙasa ce Da Zamu Iya Gina Ta Yadda Duk Muke Fata,” Inji Sanarwar.

Advertisement

Bugu Da Ƙari, Inda Ranka Na Fatan Al’ummar Musulmi Zasu Cigaba Da Aikata Ayyukan Alkhairi Da Suka Koya A Watan Ramadan, Ba Kawai A Lokacin Sallah Ba, Har Ma A Kowane Lokaci.

A Ƙarshe, Shugaban Jaridar Ya Yaba Da Ƙoƙarin Ɗaukacin Ma’aikatan Ta, Tare Da Yi Musu Addu’ar Samun Albarka Da Kariyar Ubangiji.

Advertisement

 

Allahumma Amin! Barka da Sallah!

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending