News
Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Sallah
Shahararren ɗan siyasa kuma tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar bikin Karamar Sallah.
A cikin sakonsa na taya murna, Garo ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da rayuwa bisa darussan da suka koya a watan Ramadan, kamar hakuri, yafiya, jin kai da taimakon juna.
Jaridar Inda Ranka Na Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Ƙaramar Sallah.
Ya kuma jaddada cewa azumin watan Ramadan lokaci ne da ke ƙarfafa dangantaka tsakanin bawa da Mahaliccinsa. A cewarsa, darussan da ke cikin watan Ramadan dole ne su ci gaba da wanzuwa a cikin al’umma domin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
Garo ya bukaci al’ummar Musulmi, musamman na jihar Kano, da su yi addu’o’i domin zaman lafiya da yalwar arziki. Ya kuma yi fatan Allah ya karɓi ibadun da aka gudanar a cikin watan Ramadan, ya ba kowa lafiya, da zaman lafiya, da kuma bunkasar tattalin arziki.
“Allah ya karɓi ibadunmu, ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Amin,” in ji Murtala Sule Garo.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News2 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
