News
MURNAR SALLAH: Mu Ci Gaba Da Rayuwa Cikin Zaman Lafiya Da Soyayya – Amb. Bello Sani Maitakalma
A yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da bukukuwan karamar Sallah a fadin duniya, Amb. Bello Sani Maitakalma, Sa’in Hausawan Afrika, Jarumin Arewa, Garkuwar Sarkin Malaman Abuja, kuma Shugaban rukunin kamfanin Maitakalma Global Travels, ya taya al’ummar jihar Kano da Arewacin Najeriya baki daya murnar Sallah.
Ya jaddada muhimmancin darusan watan Ramadan, musamman hakuri, yafiya, jin kai da taimakon juna, yana mai kira ga Musulmi da su ci gaba da rayuwa bisa wadannan kyawawan dabi’u.
Amb. Bello Sani Maitakalma ya bukaci matasa da su kasance masu kishin zaman lafiya, su guji duk wani abu da zai kawo tashin hankali ko rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.
Haka nan, ya yi fatan alheri ga kowa tare da addu’ar Allah ya karbi ibadun da aka gudanar a Ramadan, ya ba da lafiya, zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki a Najeriya.
Amin.
