News
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Tsawaita NYSC Zuwa Shekaru Biyu – Ministan Ilimi
A wani yunkuri na magance matsalar rashin aikin yi da kara inganta horar da matasa, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar tsawaita tsarin hidimar ƙasa (NYSC) daga shekara guda zuwa shekaru biyu.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar da Daraktan NYSC, Brigediya Janar Olakunle Nafiu, ya kai ofishinsa, inda ya jaddada cewa karin shekarar za ta taimaka wajen faɗaɗa shirin koyon sana’o’i da horon ci gaban kasuwanci ga matasa.
Gwamnatin Kebbi Ta Dakatar Da Babban Sakatare Saboda Kididdigar ‘Yan Luwadi da Madigo A Jihar
Dr. Alausa ya ce, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan matasa marasa aikin yi a kasar. Haka kuma ya yi nuni da muhimmancin tura karin malamai masu digiri zuwa yankunan karkara domin cike gibin malamai a makarantun da ke cikin waɗannan yankuna.
Sakataren dindindin na Ma’aikatar Ilimi, Mista Abel Olumuyiwa Enitan, ya tabbatar da cewa ma’aikatar tana da niyyar yin ƙarin haɗin gwiwa da NYSC domin kara inganta harkar ilimi a ƙasar.
Ministan ya kuma yaba wa kokarin NYSC wajen daƙile harkallar takardun bogi, musamman daga daliban da suka yi karatu a ƙasashen yammacin Afirka. A nasa bangaren, Brigediya Janar Nafiu, ya ba da shawarar kafa rumbun bayanai na matasan da ke karatu a ƙasashen waje domin taimakawa wajen tantance sahihancin takardunsu.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
