Connect with us

News

Gwamnatin Kebbi Ta Dakatar Da Babban Sakatare Saboda Kididdigar ‘Yan Luwadi da Madigo A Jihar

Published

on

FB IMG 1743825546263

 

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da babban sakataren ofishin fadar gwamnatin jihar Nasiru Abubakar Kigo, saboda ikirarin da yayi cewa jihohin Kebbi da Sokoto ne suka fi yawan ƴan Luwaɗi da maɗigo.

Advertisement

Wannan mataki ya biyo bayan zazzafar suka da furucin ya haifar a tsakanin al’ummar jihar, wanda ya haddasa cece-kuce da tada jijiyoyin wuya a kafafen sada zumunta da kuma tsakanin jama’a.

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Barazanar Soke Lasisin Rijiyoyin Man Da Ba Sa Aiki

Mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris, ya tabbatar da dakatarwar a ranar Juma’a, yana mai cewa an dauki matakin ne domin kare martabar jihar da kuma ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Advertisement

A cikin wata takarda da shugaban ma’aikata na jihar, Malami Shekare, ya fitar, an bayyana cewa: “A bisa ka’idar aiki da ladabi, ana dakatar da ku daga aiki har zuwa lokacin da za a kammala bincike dangane da furucin da kuka yi wanda ya saba da dabi’un al’umma.”

Furucin Kigo da ke zargin cewa Kebbi da Sokoto su ne ke dauke da mafi yawan ‘yan luwadi da madigo ya haifar da martani daga bangarori da dama ciki har da kungiyoyin addini da na al’umma, wadanda suka bukaci a dauki mataki cikin gaggawa.

Advertisement

Gwamnatin jihar ta sha alwashin gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiya da adalci acikin lamarin.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending