Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Barazanar Soke Lasisin Rijiyoyin Man Da Ba Sa Aiki

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar soke lasisin duk wasu rijiyoyin man fetur da ke hannun kamfanoni masu zaman kansu da suka gaza bunƙasa su domin amfanin tattalin arzikin ƙasa.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masana’antar mai da kamfanin IOC ya shirya a birnin Florence na ƙasar Italiya.

Advertisement

Shugaba Tinubu Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwar Shekh Dr Idris AbdulAziz 

Lokpobiri ya ce wannan matakin na da nasaba da rashin bin tsarin gwamnatin tarayya na karfafa bunƙasar fannin mai da iskar gas, inda gwamnati ke ci gaba da samar da duk wani abun da ya dace domin gudanar da ayyuka cikin tsaro da inganci.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na da niyyar haƙo ganga miliyan 2.06 a kowace rana a shekarar 2025, kuma zai zama wajibi a ɗauki matakan ladabtarwa ga dukkan kamfanonin da ke da rijiyoyin mai amma suka gaza inganta su.

Advertisement

A cewar rahoton Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC), ana haƙo ganga miliyan 1.67 a kowace rana a yanzu, abin da ke nuna akwai gibi da ya kamata a cike domin cimma burin da aka sanya gaba.

Sanarwar da mai taimaka wa Ministan kan harkokin yaɗa labarai, Mista Nneamaka Okafor, ya fitar ta tabbatar da cewa wannan gargadi ya fito daga bakin ministan a wajen taron da ya haɗa manyan kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa, inda aka jaddada buƙatar haɗin gwiwa da saurin aiki domin farfaɗo da fannin.

Advertisement

Gwamnatin ta sha alwashin aiwatar da tanade-tanaden dokar masana’antar mai, wato “haƙo mai ba dare ba rana”, domin tabbatar da cewa kowace rijiyar mai tana taka rawa wajen haɓaka tattalinarzikin ƙasa.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending