News
Gwamnatin Jigawa Ta Tilasta Wa Jami’an Tsaro Mata Sanya Hijabi A Fadin Jihar
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sabon mataki da ke ba wa jami’an tsaro mata damar sanya hijabi yayin gudanar da aikinsu. Wannan na zuwa ne bayan wani taron majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar a daren Talata.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Sagir Musa, ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya bayyana cewa gwamnati ta umarci wasu kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda uku da ke aiki a fadin jihar da su bai wa ma’aikatansu mata dama ta sanya hijabi.
A cewar kwamishinan, wannan mataki na cikin ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da yanayin aiki da ke mutunta addini, al’ada, da ‘yancin ma’aikata, musamman mata kamar yanda Jaridar PUNCH ta ruwaito
“Bada dama ga mata masu aikin tsaro su sanya hijabi zai kara musu kwarin gwiwa da natsuwa wajen gudanar da aikinsu, ba tare da tauye ‘yancinsu na addini ba,” in ji Sagir Musa.
Ya kara da cewa matakin ya biyo bayan rahoton da kwamitin tsaro na makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar ga majalisar zartarwa, inda aka jaddada bukatar mutunta dabi’u da al’adun ma’aikata mata.
Kwamishinan ya bayyana cewa kamfanonin tsaro da ke da ma’aikata 9,969 a fadin jihar, za su fara aiwatar da wannan sabon tsarin, domin inganta zaman lafiya da hadin kai a wajen aiki.
“Wannan mataki ya nuna yadda gwamnatin jihar ke dagewa wajen mutunta dokokin aikin da ke tallafa wa ‘yan kasa cikin adalci da daidaito,” in ji shi.
