News
YNAYIN ZAFI: Shugaban Essential Medical Care, Tasiu Abdallah, Yayi Kira Ga Jama’a Su Kula Da Lafiyarsu
Shugaban babbar cibiyar kula da lafiya ta Essential Medical Care, Malam Tasiu Abdallah, ya yi kira mai karfi ga al’umma dangane da yadda yanayi mai zafi ke iya shafar lafiyar jiki.
A yayin wata tattaunawa da wakilin gidan jaridar INDA RANKA, shugaban ya bayyana cewa lokaci ya yi da jama’a za su kara mayar da hankali wajen kula da lafiyarsu ta hanyar yawaita shan ruwa, cin kayan marmari, da kuma gujewa yawan fita rana ba tare da kariya ba.
2025: Za Mu Yi Aikin Hajji Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Nijeriya – Sheikh Abdullahi Sale Usman
Tasiu ya ce, “Yanayin zafi na saurin kone ruwa a jikin dan Adam, don haka yana da matukar muhimmanci mu rika yawan shan ruwa domin kare kanmu daga kamuwa da cututtuka masu nasaba da rashin ruwa a jiki.”
Ya kuma jaddada muhimmancin guje wa cizon sauro, musamman ga mata masu juna biyu, inda ya ce hakan na da matukar tasiri wajen kare lafiyar uwa da jariri daga cututtuka irinsu zazzabin cizon sauro. Ya bukaci iyaye mata da su kasance masu shiga dakunan sauro ko amfani da gidajen kariya daga sauro, musamman a wannan lokacin zafi da sauro ke yawan fitowa.
Kazalika, shugaban ya bayyana cewa cibiyar Essential Medical Care ta kammala tsare-tsare domin karfafa gwiwar al’umma wajen samun kulawar lafiya ta inganci a farashi mai sauki, tare da bayar da tallafi ga wadanda ke da rubutaccen magani daga wasu asibitoci.
Cibiyar ba ta tsaya a nan ba, domin ta kafa reshen Tasiu Abdallah Pharmaceutical Sales, wanda ke tallafa wa asibitoci, dakunan shan magani (Pharmacy) da Chemist da magunguna a farashin sari domin saukaka rayuwa.
Wannan bayani ya fito ne bayan wata ziyarar da wakilin jaridar Inda Ranka ya kai a babban ofishin cibiyar da ke kan titn Maiduguri, Hotoro, kusa da ARTV da Salik Plaza, inda ake ci gaba da shirye-shirye na bude sabon reshe mai girma a yankin.
“Muna kokari kullum wajen ganin al’umma sun samu lafiya mai dorewa, kuma mu taimaka musu ta hanyar saukaka hanyoyin samun magani da kulawa daga kwararru,” in ji Tasiu Abdallah.
