Connect with us

News

Saudiyya Ta Hana Ɗaukar Hoto A Manyan Guraren Ibada

Published

on

Dutsen Arfa

A yau Alhamis, 9 ga watan Zulhijja, mahajjata fiye da miliyan 1.5 daga sassa daban-daban na duniya ne suka hallara a filin Arfa domin gudanar da tsayuwar Arfa, wadda ita ce rana mafi muhimmanci a cikin ranakun aikin hajji.

A daidai wannan lokaci, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar da sabuwar doka da ta haramta ɗaukar hoto, naɗar bidiyo, da kuma bayyana kowace alama ko kalma da ke da nasaba da siyasa a manyan guraren ibada, ciki har da Masallacin Harami a Makka da Masallacin Annabi (SAW) a Madina.

Advertisement

‎Yaɗa Bayanan Ƙarya Da Jita-Jita Sun Rura Wuta A Lokacin Yakin Basasa ‎ ‎ ‎ ‎ — Obasanjo

Sanarwar ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin kare tsarkin wuraren ibada da tabbatar da nutsuwa ga mahajjata, tare da hana duk wani abu da zai iya janyo cikas ga gudanar da ibada.

A cewar hukumomin Saudiyya, an ƙaddamar da amfani da fasahar zamani kamar Artificial Intelligence (AI) da jiragen sama marasa matuki (drone) don tabbatar da tsaro da lafiya ga mahajjata a wannan lokaci mai muhimmanci.

Advertisement

Wannan mataki ya biyo bayan yadda wasu mahajjata ke mayar da guraren ibada wajen ɗaukar hotuna da bidiyo, maimakon mayar da hankali kan ibada, abin da hukumomin ƙasar suka bayyana a matsayin saba wa kyawawan ɗabi’un aikin hajji.

A halin yanzu, rahotanni daga filin Arfa na nuna cewa zafin rana ya kai digiri 41 a ma’aunin Celsius, lamarin da ya sa mahajjata ke ta shan ruwa da amfani da lemo domin kare lafiyar jikinsu daga illar zafi.

Advertisement

 

FRI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending