News
Jami’an ‘yan sanda Sun Cafke Wasu Mutune Uku Da Ake Zargi Da Satar Mota Kano
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da hannu a satar mota, tare da kwato wata mota da aka sace aka sayar da ita a Jamhuriyar Nijar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025.
Yaduwar Al’adar ‘Signing Out’ A Makarantun Sakandare: Gazawar Iyaye Ko Hukumomi?
Sanarwar ta bayyana cewa ɗaya daga cikin wanda ake zargi, Shamsu Yusuf wanda aka fi sani da “Chitta”, ya saci motar ne a unguwar Gadon Kaya da ke cikin birnin Kano. Lamarin ya faru ne lokacin da aka ba shi mota domin yin gwajin tuki da sunan zai saya.
Bayan ya yi diba da motar, sai ya tsere da ita zuwa jihar Katsina, inda rundunar ta ce an cafke shi tare da wasu mutum biyu da ake zargin suna da hannu a lamarin.
‘Yan sanda sun ce motar da aka kwato ita ce Toyota Corolla, samfurin 2013, wadda aka tabbatar da cewa an riga an sayar da ita zuwa Jamhuriyar Nijar.
A cewar SP Kiyawa, bincike yana ci gaba domin gano sauran motoci da ake zargin “Chitta” ya saci a baya da kuma bankado sauran abokan aikinsa.
