Connect with us

News

Gwamna Ogbonna Na Ebonyi Ya Dakatar Da Kwamishinoni 25 Da Wasu Manyan Jami’an Gwamnati 60

Published

on

images (2)

Gwamnan Jihar Ebonyi, Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru, ya dakatar da kwamishinoni 25 da masu taimaka masa na musamman guda 38, tare da manyan sakatarorin ma’aikatu 22, bisa gazawarsu na halartar wani muhimmin taro da gwamnatin jihar ta kira.

Wannan mataki da gwamnan ya dauka na dakatarwar wata guda ba tare da biyan albashi ba, na zaman martani kan abin da ya bayyana a matsayin nuna halin ko-in-kula da sakaci wajen gudanar da aikinsu na gwamnati.

Advertisement

Yansanda Sun Gano Gawar Dan Jarida Mai Daukar Hoto Da Makwabcinsa Ya Hallaka  

A wata sanarwa da aka fitar a daren Litinin daga ofishin gwamnan, an umarci duk jami’an da dakatarwar ta shafa da su dakatar da sanya hannu ko amincewa da duk wata takarda da ke da nasaba da gwamnatin jihar, har sai lokacin da wa’adin dakatarwar ya cika.

Haka kuma, an umurci dukkan kwamishinonin da abin ya shafa da su mika ragamar ofisoshinsu ga manyan sakatarorin ma’aikatunsu, domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Advertisement

Matakin na Gwamna Ogbonna dai na zaman na farko da aka taba dauka a jihar Ebonyi kan irin wadannan manyan jami’an gwamnati, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin jihar, tare da jan hankalin sauran ma’aikata da ke karkashin gwamnatin jihar da su dauki nauyin aikinsu da muhimmanci.

Majiyoyi daga cikin gwamnatin jihar sun bayyana cewa, taron da jami’an suka gaza halarta na da matukar muhimmanci wajen tsara manyan ayyuka da shirye-shiryen cigaban jihar.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending