News
Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Kafin Tsayawa Dillalin Kwayoyi A Kotu —Rahoton DSS
Rahoton sirri daga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ya zargi Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, da karɓar cin hancin Dala $30,000 domin tsayawa wani shahararren dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, a matsayin surety a kotu.
Wannan batu ya fito fili ne a cikin rahoton binciken da DSS ta mika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda hukumar ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya tabbatar da wannan zargi.
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Ta Kori Dalibai 57 Kan Laifin Satar Amsa
Rahoton ya kuma bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakin dakatar da kwamishinan daga mukaminsa, domin bai kamata irin wannan zargi mai nauyi ya ci gaba da hawa kafadarsa ba, yana wakiltar gwamnati.
Kwamishina Ibrahim Namadi, wanda aka ruwaito cewa ya taɓa fuskantar tuhumar damfara a shekarar 2013, ya samu wannan mukami ne bisa kusancin sa da jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Kano ne.
A wani mataki na gaggawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin bincike domin nazarin cikakken bayani kan zargin da ake wa kwamishinan, tare da bayar da umarni ga kwamitin da ya kammala rahoton sa cikin mako guda.
Wata majiya daga fadar gwamnatin jihar ta bayyana cewa gwamnan ya fusata matuka kan yadda wani daga cikin masu rike da mukamai a gwamnatinsa zai yi cudanya da masu safarar miyagun kwayoyi — abin da ke barazana ga tsare-tsaren yaki da ta’ammali da kwayoyi da gwamnati ke yi, musamman dangane da batun kama Sulaiman Danwawu.
Majiyar ta kara da cewa, “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki wannan batu a matsayin kalubale ga doka da oda, tare da bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai bata sunanta ko ya dagula kokarinta na farfado da rayuwarmatasa ba.”
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
