Connect with us

News

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Ta Kori Dalibai 57 Kan Laifin Satar Amsa

Published

on

Uni Jos Students

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 bayan kama su da laifin satar amsa da kuma aikata maguɗi a lokacin jarabawa.

Kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a safiyar Asabar, inda ta ce majalisar jami’ar ta amince da hukuncin ne bayan karɓar rahoton kwamitin ladabtarwa da ya gudanar da bincike kan laifukan da suka shafi jarabawa.

Ambaliya Ta Halaka Mutane 165, Yayin Da Wasu 82 Suka Bace A Bana – NEMA

Haka kuma, jami’ar ta dakatar da wasu ɗalibai biyar na tsawon shekara guda, yayin da aka fitar da takardar gargaɗi ga wasu biyu da aka samu da aikata laifin satar amsa ko maguɗin jarabawa.

Bugu da ƙari, an dakatar da wasu ɗalibai biyar na tsawon shekarar karatu biyu, tare da soke dukkan jarabawarsu da aka gano sun aikata laifi a kansu.

Jami’ar ta jaddada cewa ba za ta lamunci satar amsa, maguɗi ko wata irin rashin ɗa’a daga cikin ɗalibanta ba, tana mai cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri don kare darajar tsarin karatu da martabar jami’ar.

 

Advertisement

SOLACEBASE

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending