News
Jami’an NDLEA Sun Kama Taba Wiwi Mai Nauyin Kilo 112 A Kano Bayan Haɗarin Mota
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama bulo 150 da buhuna uku na tabar wiwi mai nauyin kilo 112 a kusa da Gadar Tamburawa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano, bayan wani haɗarin mota da ya auku ranar Asabar, 6 ga Satumba, 2025.
Wata sanarwa da kakakin hukumar a Kano, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar ranar Alhamis ta ce jami’an hukumar da ke sintiri sun isa wurin haɗarin bayan motar Golf ta yi karo da babbar mota.
Ƙungiyar Likitoci Sun Bai Wa Gwamnatin Tarayya Sa’o’i 24 Kafin Tsunduma Yajin Aiki
Sanarwar ta ce jami’an sun ceto direban Golf da fasinja daga cikin motar. Sai dai nan da nan fasinjan ya yi ƙoƙarin tserewa, amma jami’an suka cafke shi.
Binciken farko ya gano bulo 150 da buhuna uku na tabar wiwi a cikin Golf ɗin.
Direban, wanda ya samu raunuka a jiki, ya shaida wa jami’an cewa shi ne wakilin mai kayan, kuma ya sha yin irin wannan safarar a Kano da wajen ta. Ya ƙara da cewa ya yi amfani da hanyar “one way” domin guje wa shingen binciken NDLEA.
Rahoton ya ce yanzu haka direban na karɓar magani yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike. Rahotanni kuma sun nuna cewa direban babbar motar da aka yi karon da shi ya samu karaya.
Hukumar NDLEA a Kano ta ce za ta ci gaba da ƙoƙari wajen magance safarar miyagun ƙwayoyi da kuma gurfanar da masu hannu a gaban kotu. Ta kuma yi kira ga jama’a da su guji shiga irin wannan laifi tare da bayar da rahoton duk wani motsi na miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta yabawa jajircewar jami’an sintirin da suka gudanar da aikin ceto da cafke waɗanda ake zargi, tare da jinjinawa shugaban hukumar na ƙasa, Janar Mohammed Buba Marwa (rtd), bisa tsare-tsaren da suka ƙara inganta ayyukan hukumar a faɗin ƙasar.
