News
Ƴansanda Sun Kama Wani Dattijo Mai Shekara 63, Bisa Zargin Satar Babur A Neja.
Rundunar Ƴansanda ta jihar Neja ta kama wani dattijo mai shekara 63, bisa zargin satar babur kirar Bajaj a ƙauyen Tugan-Kawo da ke cikin ƙaramar hukumar Kontagora.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an cafke shi ne a lokacin da ya ke ƙoƙarin satar babur ɗin, inda jami’an tsaro suka same shi da makullai da dama da ake zargin yana amfani da su wajen buɗe babura.
Wani Matashi Ya Ƙwaƙwule Idon Kanwar Sa Yar Shekara 7 A Bauchi
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, yana mai cewa an kama wanda ake zargin ne tare da taimakon ƴan banga.
Abiodun ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa bayan kama shi, kuma daga baya an gano mamallakin babur ɗin da aka yi ƙoƙarin satarwa
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News17 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
