Connect with us

Labarai

An Tura Wani Matashi Gidan Kurkuku Bayan Ya Yaga Hotan Shugaban Kasa

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wani matashi mai suna Mouhamadou Bachir Syll a Senegal ya shiga hannun hukuma bayan da ya yaga hoton shugaban kasa, Bassirou Diomaye Faye, lamarin da ya janyo cece-kuce a kasar.

Ofishin ‘yan sanda na tsakiyar birnin Saint-Louis ya kammala bincike kan lamarin, inda aka gurfanar da Syll gaban kotu a safiyar Juma’a bisa zargin cin fuska ga shugaban kasa da kuma zagon kasa ga Shugaban a bainar jama’a.

Bayan gabatar da rahoton farko, babban jami’in shari’a, Baye Thiam, ya bukaci a bude cikakken binciken shari’a, inda ya nemi a fitar da takardar cafke matashin.

Daga nan ne alkalin  Babbar Kotun Saint-Louis ya tuhumi matashin, sannan aka tura shi Gidan kurkuku. Ana sa ran zai yi daren farko a gidan yari yayin da shari’a ke ci gaba.

A cikin ‘yan kwanakin baya, wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna matashin yana fasa hoton shugaban kasa a matsayin “dan kasa mai kishin ƙasa”, inda kuma ya yi wasu maganganu na rashin kunya da cin fuska kan shugaban. Wannan bidiyo ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin al’umma.

 

Advertisement

Seneweb

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending