News
An Samu Tashin Gobara Sau 5 Cikin Sa’o’i 24 A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce an samu tashin gobara sau biyar a sassa daban-daban na birnin Kano cikin sa’o’i 24, daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Janairun 2026.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya ce gobarorin sun tashi ne a unguwannin Badawa, Ɗanladi Nasidi, Kasuwar Singa, Titin Independence da Ja’en.
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Layin Dogo A Birnin Kano Na Naira Tiriliyan 1
A cewarsa, ba a samu asarar rai ko guda ba a sanadin gobarorin, sai dai an samu asarar dukiya mai yawa, duk da gaggawar da jami’an hukumar suka kai wuraren da lamarin ya shafa.
Sanarwar ta ce gobara ta farko ta tashi ne da misalin ƙarfe 4:17 na asuba a unguwar Badawa da ke karamar hukumar Nassarawa, inda wata gobara ta shafi wani ƙaramin shagon sayar da magunguna. Jami’an tashar Dakata sun samu nasarar shawo kan lamarin kafin ya bazu.
Gobarar ta biyu kuma ta faru ne da misalin ƙarfe 1:20 na rana a layin Maiduguri, cikin gidajen Ɗanladi Nasidi, inda wutar ta tashi a wani fili da ake amfani da shi wajen girke na’urorin sadarwa na kamfanonin MTN da Airtel.
A Kasuwar Singa, kusa da Bello Dandago, gobara ta tashi da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, inda wata motar kwantena ɗauke da kayan Indomie ta kama da wuta, lamarin da ya shafi wasu sassan motar da kayan da ke cikinta.
Sanarwar ta ƙara da cewa gobara ta huɗu ta tashi ne a Titin Independence, kusa da gidan rediyon Aminci, inda wuta ta shafi wani fili da ake sarrafa ƙarafa, tare da lalata injuna da janareto, da kuma shafar sandunan fitilar titi da na’urorin hasken rana.
Gobarar ta biyar kuma ta faru ne a Ja’en, kusa da Ajawa, inda wani gidan zama mai ɗakuna biyu da kicin ɗaya ya samu ɗan lalacewa sakamakon wutar, kafin jami’an tashar Sharada su shawo kan lamarin.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta shawarci al’umma da su riƙa kashe na’urorin lantarki idan ba a amfani da su, su guji haɗin lantarki ba bisa ka’ida ba, tare da adana abubuwan da ke saurin kamawa da wuta yadda ya kamata.
