News
An Kwashe Sama Da Mutum 200 Masu Larurar Kwakwalwa Daga Tituna — Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta fara wani shiri na musamman na kwashe mutanen da ke fama da larurar ƙwaƙwalwa daga tituna da unguwannin birnin KanoKano, domin ba su kulawar lafiya tare da rage matsalolin tsaro.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) ta tabbatar da cewa sama da mutum 200 ne aka riga aka kwashe, inda aka killace su domin ba su magani da kulawar da ta dace, kafin a mayar da su zuwa garuruwansu ko iyalansu.
DSS Ta Gurfanar Da Abubakar Malami Da Ɗansa A Gaban Kotu Kan Zargin Tallafa Wa Ta’addanci
Babban Sakataren hukumar, Abdullahi Isyaku Kubarachi, ya shaida wa manema labarai cewa aikin na daga cikin ayyukan yau da kullum na SEMA, kuma ana aiwatar da shi ne da daddare tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Ya ce an fara aikin ne a ƙananan hukumomi huɗu da ke cikin birnin Kano, bisa umarnin gwamnatin jihar, kafin daga bisani a faɗaɗa shi zuwa sauran sassan jihar.
A cewarsa, manufar wannan shiri ita ce ba wa mutanen da ke fama da larurar ƙwaƙwalwa kulawa ta jinƙai a matsayinsu na ‘yan Adam, tare da taimaka musu su koma cikin iyalansu da al’umma yadda ya dace.
Hukumar ta SEMA ta kuma buƙaci al’umma da su rika bai wa jami’an tsaro rahoton mutanen da ke fama da matsalar ƙwaƙwalwa, musamman idan halayensu na iya zama barazana ga tsaro.
Masana na bayyana cewa matsalar larurar ƙwaƙwalwa na ƙara ta’azzara a sassa da dama na Najeriya, inda rashin kulawa da talauci ke ƙara dagula halin da masu fama da ita ke ciki.
