Connect with us

News

DSS Ta Gurfanar Da Abubakar Malami Da Ɗansa A Gaban Kotu Kan Zargin Tallafa Wa Ta’addanci

Published

on

images (2)

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Ƙasa, DSS, ta gurfanar da tsohon Antoni Janar na Ƙasa, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdulaziz Malami, a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuma mallakar makamai ba tare da izini ba.

An gabatar da su gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik a ranar Talata, inda aka karanta musu tuhume-tuhume shida, amma dukansu sun musanta zarge-zargen da ake yi musu.

Advertisement

Kotun Kano Ta Sanya 15 Ga Afrilu Don Ci gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Almundahana

Lauyan gwamnatin tarayya, C. S. Eze, ya roƙi kotu da ta ɗage sauraron shari’ar tare da ci gaba da tsare waɗanda ake tuhuma a hannun DSS har zuwa kammala shari’ar. Sai dai lauyan karewa, Shuaibu Aruwa, ya nemi beli, yana mai cewa an shafe kusan makonni biyu ana tsare da su, tare da jaddada dalilan jinƙai.

Advertisement

Alƙaliya Joyce Abdulmalik ta umurci ɓangaren karewa da su gabatar da rubutacciyar takardar neman beli, sannan ta ɗage shari’ar zuwa 20 ga Fabrairu domin ci gaba da sauraro.

A cikin tuhumar da aka gabatar, gwamnatin tarayya na zargin Malami da cewa a Nuwamba 2022, ya ƙi gurfanar da wasu da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci, duk da cewa an tura fayilolin shari’arsu zuwa ofishinsa a lokacin da yake Antoni Janar, abin da gwamnati ke cewa ya sabawa Dokar Hana Ta’addanci ta 2022.

Advertisement

Haka kuma, ana zargin Malami da ɗansa da mallakar bindiga kirar Sturm Magnum da harsasai, ba tare da lasisi ba, waɗanda aka ce an same su a gidansu da ke Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, a watan Disambar 2025 — zarge-zargen da ke ƙarƙashin tanade-tanaden Dokar Makamai ta Ƙasa.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending