Connect with us

News

Kotun Kano Ta Sanya 15 Ga Afrilu Don Ci gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Almundahana

Published

on

Babbar Kotun Jihar Kano ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, tare da wasu mutane, kan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Ganduje na fuskantar tuhume-tuhume 11 ne tare da matarsa, Hafsat Umar, waɗanda suka haɗa da zargin karɓar rashawa, haɗin baki, almundahana da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai biliyoyin naira.

NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar Na Shekarar 2025 

Sauran mutanen da ake tuhuma a shari’ar sun haɗa da Abubakar Bawuro, Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, yayin da ake zargin kamfanoni uku – Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da Lasage General Enterprises Ltd – da hannu a lamarin.

A zaman kotun na baya-bayan nan, lauyan gwamnati Victor Oni ya sanar da kotu cewa gwamnati na da shirin ci gaba da shari’ar, tare da buƙatar da ya shigar tun 24 ga Nuwamba, 2025, domin neman izinin gabatar da ƙarin hujjoji.

A ɓangaren masu kare kai kuwa, lauyar Ganduje, Lydia Oluwakemi Oyewo, ta bayyana cewa sun shigar da buƙatar dakatar da shari’ar tun 17 ga Yuli, 2025, yayin da lauyoyin sauran waɗanda ake tuhuma suka ce suna da buƙatu da ƙorafe-ƙorafe daban-daban da ke gaban kotu, ciki har da neman ƙarin lokaci.

Advertisement

Kotun ta ce za ta saurari dukkan buƙatun da ke gabanta a ranar da ta ɗaga zaman, kafin yanke shawarar matakin da za a ɗauka na gaba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending