Connect with us

News

Gobara Ta Kone Shaguna 85 A Kasuwar Yan Katako Da Ke Rijiyar Lemo A Kano 

Published

on

Aƙalla shaguna 85 ne suka ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi a wasu sassan kasuwar Ƴan Katako da ke Rijiyar Lemo, a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta jihar Kano, a safiyar Laraba.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:28 na Asuba, bayan da ta samu kiran gaggawa daga Kabiru Nafi’u wanda ya sanar da tashin gobara a kasuwar.

Advertisement

Kwankwasiyya Ta Karyata Zargin Amurka Kan Sanata Kwankwaso

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, ya ce: “Da isar jami’anmu, sun tarar da kasuwar katako mai girman kafa 500 da 500 tana ci da wuta. Kimanin manyan shaguna 30 da kuma ƙananu 55 sun ƙone gaba ɗaya.”

Advertisement

Ya ce sun tura jami’an kashe gobara daga tashoshin Dawanau, Rijiyar Zaki da Bompai nan take, inda aka yi amfani da motocin kashe gobara uku domin shawo kan gobarar.

Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending