Connect with us

News

Yankuna 178 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Kano – NEMA ‎

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi gargaɗin cewa yankuna 178 da ke cikin ƙananan hukumomi 28 na Jihar Kano na iya fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a lokacin daminar shekarar 2026.

‎An bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin ƙaddamar da shirye-shiryen tunkarar damina da kuma rage haɗurran bala’o’i da ka iya afkuwa a jihar.

Advertisement

Amarya Ta Hallaka Uwargida Kan Takaddamar Rabon Naman Sallah

‎Rahotanni da NEMA ta gabatar sun nuna cewa ƙananan hukumomin da ke cikin jerin wuraren da ambaliya za ta iya shafa sun haɗa da Ajingi, Bagwai, Bebeji, Bichi, Bunkure, Dala, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Fagge, Gabasawa, Garun Malam, Gaya, Gwale, Kabo, Karaye, Kiru, Kunchi, Tsanyawa, Kura, Madobi, Rano, Rimin Gado, Sumaila, Takai, Tofa, Tudun Wada, Ungogo da Warawa.

Advertisement

‎A yayin taron, Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta riga ta fara aiwatar da wasu matakan kariya domin rage yiwuwar afkuwar ambaliya, ciki har da kwashe magudanan ruwa, cire gine-ginen da suka toshe hanyoyin ruwa da kuma shirin dasa bishiyoyi miliyan 10 a sassa daban-daban na jihar.

‎Haka kuma, gwamnatin da NEMA sun yi kira ga al’umma, musamman mazauna yankunan da ke cikin haɗari, da su ɗauki gargaɗin da muhimmanci tare da bin shawarwarin hukumomi domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Advertisement

‎Sun jaddada cewa haɗin kan jama’a da bin matakan kariya na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage asarar da ambaliya ke haddasawa a lokacin damina.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending