Connect with us

News

ADC Na Neman Raba Gawuna Da Tsarin NDC Kwankwasiyya Bayan Yimasa Tayin Takarar Gwamnan Kano A 2027

Published

on

IMG 20260606 232946 154

Jam’iyyar ADC ta kara kaimi wajen jawo tsohon dan takarar gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, domin ya tsaya takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar a zaben 2027.

Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa manyan jiga-jigan ADC na tattaunawa da makusantan Gawuna domin shawo kansa ya amince da tikitin gwamna na jam’iyyar. Rahotanni sun ce jam’iyyar ta yi alkawarin ba wasu daga cikin magoya bayansa tikitin takarar kujerun majalisar dokokin jihar da ta wakilai, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan kudi idan ya amince ya shiga takarar.

Advertisement

“Rahoton ‘The Historica Nigeria’ Ya Jawo Matakin Gwamnati yayin Da Aka Dakatar Da Sare Bishiyoyi A ARTV

An ce tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da tsohon jakada Faruk Yabo na daga cikin wadanda ke jagorantar yunkurin shigar da Gawuna cikin jam’iyyar.

Advertisement

Ko da yake Gawuna ya sha bayyana biyayyarsa ga tafiyar Kwankwasiyya, majiyoyi sun ce matsin lambar da ADC ke yi tare da tayin siyasar da ta gabatar ya sa ana sake nazari a sansaninsa.

Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa har yanzu shugabancin ADC na kasa bai sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan Kano tsakanin Ibrahim Khalil da Ibrahim Little, inda wasu ke ganin jinkirin na da nasaba da kokarin cimma yarjejeniya da Gawuna.

Advertisement

Gawuna, wanda ya taba zama mataimakin gwamnan Kano kuma dan takarar gwamna na All Progressives Congress a zaben 2023, na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan jagororin adawa a jihar.

Masu sa ido kan harkokin siyasa sun bayyana cewa har yanzu yana da dimbin magoya baya a fadin Kano, lamarin da ya sa jam’iyyu ke kallonsa a matsayin babban kalubale ga gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, a zaben 2027.

Advertisement

Zu zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Gawuna ko jami’an ADC kan tattaunawar da ake cewa na gudana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending